Daga kasar Suriya bayan ta nakalto daga majiyar aljazira cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: kasar suriya ta yi Allah wadai da mayar da masallacin Ibrahima karkashin mallakarta da kuma mamaye kabarin babban sahabin nan Bilal .
Har ila yau ta bayyana cewa wannan mataki ne na takwalar fada da ta'addanci da hakan ke tabbatar da mummunar manufar haramtacciyar kasar Isra'ila da yahudancin Sahayoniya na neman tada zaune tsaye da karyawa inda babu gaba da take duk wata doka ta kasa da kasa da na kare hakkokin dan adam da addinansu.
543678