IQNA

Kablan Ya Bukaci Hadin Kan larabaw ya Mayar Da Martani Kan HKI

15:24 - February 25, 2010
Lambar Labari: 1890589
Bangaren siyasa da zamantakewa' ayatullahi Kablan mukaddashin majalisar koli ta yan shi'a a Labanon ya yi Allah wadai da matakin nuna wariya da ta'addancin haramtacciyar kasar Isra'ila na mallake masallacin Ibrahima (AS) da kabarin Bilal .
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ce daga reshenta na kasar Suriya ta watsa rahoton cewa; zamantakewa' ayatullahi Kablan mukaddashin majalisar koli ta yan shi'a a Labanon ya yi Allah wadai da matakin nuna wariya da ta'addancin haramtacciyar kasar Isra'ila na mallake masallacin Ibrahima (AS) da kabarin Bilal . Ya kuma jaddada wajibcin kasashen larabawa al'ummominsu da gwamnatocinsu da sauran musulmin duniya su hada kai da tashi tsaye ba kasawa wajen ganin sun kawo karshen wannan ta'addanci da haramtacciyar kasar Isra'ila ked a zummar yi.


543586
captcha