Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta daga Mashhad ta watsa rahoton cewa: Maulawi Ishak Madani mai bawa shugaban kasar Iran Shawara kan harkokin Ahlul Sunna a lokacin wani taro na tunawa da zagayowar irin wannan rana ta haifuwa fiyayyen halitta Annabi Muhammad dan Abdullahi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi ya bayyana cewa: a yau makiya Musulunci a fadin duniya na ta kokarin ganin sun haddasa da kawo sabani da rikici a tsakanin malaman addinin Musulunci tare da yin kira ga malaman Musulunci da su yi takatsantsan kan wannan matsala da maidawa kura aniyarta cikin hikima da nucuwa.
546735