Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, cibiyar kula da harkokin bayar da horo kan ilmomin addinin musulunci a kasar Turkiya ta fara aiwatar da wani shiri na horas da malaman kasar. Bayanin ya kara da cewa yanzu haka an fara gudanar da wannan shiri, wanda ke samun halar daruruwan malamai da masu wa'azi daga sassa daban-daban na kasar. Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana cewa gudanar da irin wannan taro na da matukar muhimmanci ga malamai, domin hakan zai ba su damar kara iliminsu na isar da sako ga sauran musulmi. Daga cikin wadanda suke halartar taron har da babban daraktan cibiyar a Istanbul.547986