Bangaren al'adu da fasaha; a kasar Turkiya za a kaddamar da wata fim da ke bayani kan bakin zaluncin yahudawan sahayoniya kan Palasdinu da mamayen da suke yi masu.
Daga reshenta da ke kasar Turkiya ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Al'alam ta watsa rahoton cewa; a kasar Turkiya za a kaddamar da wata fim da ke bayani kan bakin zaluncin yahudawan sahayoniya kan Palasdinu da mamayen da suke yi masu. A cikin wannan fim din za a yi bayani dalla-dalla kan ta'addancin yahudawan sahayoyi yan mamaye kan fararen hula Palsdinawa dad a kuma abubuwa da suka faru a cikin tarihi ta hanyar nuna hotuna a fili karara.An yi hassashe cewa a cikin wannan fim din za a kashe kudi kimanin dola miliyon goma kuma yana daya daga cikin fim da aka kayata aikinsa da kuma kamfanonin fina-fina da hadin guiwar gidajen talbijin na kasar Turkiya.Wannan fim na nuni da yadda kasar Turkiya ke adawa da yadda sojojin Amerika da Haramtacciyar kasar Isra'ila ke kaiwa sauran kasashe hare-hare.
548685