Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, An bude wata babbar cibiyar koyar da karatun kur'ani mai tsarki a kasar Yeman, wadda za ta rika gudanar da ayyuaknata daga birnin San'a fadar mulkin kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa, wasu daga cikin wadanda suka halarci taron na jiya sun bayyana cewa da dama cikin jami'ai na ma'aiktar kula d aharkokin addinin musulunci ta kasar sun halarci zaman taron bude wannan babbar cibiya. 548195