Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta ZeeNews ta watsa rahoton cewa; ; hanyar magance duk wata matsala dad an adam ke fuskanta ita ce riko da Kur'ani mai girma kuma nauyi ne ga musulmi su yi aiki da kur'ani wajen isa ga sa'ada. Rahman Khan mukaddashin shugaban hadin guiwar lardunan Indiya a jiya ne sha biyar ga watan Isfand a wani taro na neman hanyoyin dake magana kan rayuwar zamantakewa mai inganci a cikin Kur'ani a Haidar Aba na kasar Indiya ya yi wannan bayani.
549193