Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Aljazira Net ta watsa rahoton cewa; A kasar Jamus ne hukumomin musulmi za su gudanar da taronsu na shekara shekara da mahukumtan wannan kasa suka daukin nauyin gudanarwa. Kuma Tomas Domizyir ministan da ke kula da harkokin cikin gida a Jamus kan wannan labari ya bayyana cewa: amincewa da addinin Musulunci a matsayin addinin dab a za a iya rabawa da al'ummar kasar jamus ba kan haka ne suka sanya koyar da shikashikan addinin Musulunci a makarantun hukuma da kuma tarbiyartar da malaman masallatai a jami'o'in Jamus da kuma sauran lamura.
550586