Hujjatul Islam Muhammad Hasan Wahidi mai kula da ofishin yada al'adun Iran a kasar Malaishiya a wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhurioyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: aiki da kuma dogaro da ma'anawiya ciko ne na al'adu kuma yana nufin tushen addini da Irfani kuma da suka samo asali daga Kur'ani da sunnar ma'aikin Allah (SWA). Kuma ya kara da cewa duk lokacin da muka kara kusantar kur'ani muna kara fahimtar Kur'ani da kara karfin imani da ma'anawiya ta dukan bangarorin rayuwa ta zamantakewa da dai sauransu.
551086