Bangaren al'adu da fasaha; a kasar Jodan Tuni aka fara aiki da tsarin sa ido kan kamfanoni da muassisoshin Umra a wannan kasa.
Daga reshenta da ke kasar ta Jodan cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar Aldastur da ke fitowa a wannan kasa ta watsa rahoton cewa a kasar Jodan Tuni aka fara aiki da tsarin sa ido kan kamfanoni da muassisoshin Umra a wannan kasa. Kuma ma'aikatar da ke kula da harkokin addini a wannan kasa ce kula da duk wani mataki da aka amince da shi a lokacin kaddamar da wannan shiri da tsari na sa ido.
550763