Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Aswatul Iraki ta watsa rahoton cewa; ; Hashim Isma'il Aljaza'iri mahardacin kur'ani daga lardin Misan na kasar Iraki ne ya lashe kyautar farko da aka yi tanadi a gasar kur'ani ta kasa da kasa a kasar Indiya. Kuma Ali AbdulWahid mai kula da bangaren watsa labarai nay an shi'a a lardin Misan na kasar Iraki wanda a ranar ashirin ga watan Isfand a wata tattaunawa da manema labaraii y ace ya samu wannan matsayi ne daga cikin maharda kur'ani talatin daga kasashe daban daban na duniya.
551576