Bangaren siyasa da zamantakewa; Kasar Suriya ta bukaci kasashen larabawa da su zama tsintsiya daya da hada kai guri guda domin kalubalantar wuce gona da irin haramtacciyar kasar Isra'ila kan Palasdinawa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna daga reshenta da ke kasar Suriya bayan kuma ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta gwamnatin wannan kasa Sana ta watsa rahoton cewa; Kasar Suriya ta bukaci kasashen larabawa da su zama tsintsiya daya da hada kai guri guda domin kalubalantar wuce gona da irin haramtacciyar kasar Isra'ila kan Palasdinawa. Bayanin ya nuna takaicinsa a fili kan yadda ake zaluntar yan uwansu musulmi kuma larabawa Palasdinu amma sun kasa tabuka komi a kokarin kawo karshen wannan cin zalin da haramtacciyar kasar Isra'ila ke nuna masu a fili karara.
552045