Bangaren kasa da kasa; kakakin cibiyar yaki da masu bata sunan addini da ke karkashin kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta nuna fushinta a fili kan yadda a kasar Suidin aka sake yin batanci kan ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da Alayan gidansa tsarkaka da Lars Vilks dan kasar ya yi inda jaridu uku na kasar suka watsa Dagens Nyheter,Exressen,Sydsvenska Dagbladet da kuma sauran radiyoyi da Talbijin na wannan kasa.
Cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta kungiyar hadin kan kasashen musulmi OCI ta watsa rahoton cewa; kakakin cibiyar yaki da masu bata sunan addini da ke karkashin kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta nuna fushinta a fili kan yadda a kasar Suidin aka sake yin batanci kan ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da Alayan gidansa tsarkaka da Lars Vilks dan kasar ya yi inda jaridu uku na kasar suka watsa Dagens Nyheter,Exressen,Sydsvenska Dagbladet da kuma sauran radiyoyi da Talbijin na wannan kasa. Rashin mataki na azo a gani da kasashe da gwamnatocin musulmi suka kasa dauka kan wannan cin fuska shi ne babban dalilin day a sa jaridu day an siyasa a kasashen turai ke ci gaba da cin zarafi kan addini da ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka.
552617