IQNA

Za A Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Kan Sheikh Tusi Karo Na Sha Uku

Bangaren nazari da ilimi; Jami'ar Almustapha (SWA) al'alami za ta gudanar da taron kasa da kasa kan sheikh Tusi karo na sha uku.
Auliya'a Sha'abani sakataren tsara wannan taro na kasa da kasa karo na sha uku kan Sheikh Tusi a wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna daga birnin Qum ta watsa rahoton cewa; jami'ar almustapha (SWA) al'alami ta dauki dawainiyar gudanar da wannan taro inda za a yi bayani kan rayuwar wannan bawon Allah da kuma rawar day a taka ta fuskoki dabandaban na ilimi da addini da zamantakewa.

551970