Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta IRCICA ta watsa rahoton cewa; a yankin da ke tsakanin ruwan Valga da na Ural za a gudanar da taron kasa da kasa karo na hudu kan wayewar addinin Musulunci . wannan taro ya shafi harkokin tarihi da fasaha da al'adu da hukumar da ke kula harkokin al'adu ta kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta shirya. Kuma burin gudanar da wannan shi ne kara fadada harkokin addini da addu a wannan yanki da kuma kare su.
555096