Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga elmoudjahid ta watsa rahoton cewa; Sheikh Bu Umran shugaban komitin koli na Musulunci a Aljeriya ya jaddada cewa dokokin komitin koli na musuluni a wannan kasa syn yi daidai da fadar kur'ani. Ya kara da cewa; kowa yanada hakkin bayyana akidarsa amma babu wanda yake da hakkin cin mutuncin addini da abubuwan da addini ke girmamawa kuma babu wanda yake musun cewa al'ummar Aljeriya musulmi ne kuma dukan juyin juya halin da al'ummar Aljeriya suka yi yaki ne na yanci da sunan Musulunci.
555086