Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga Saphirnews ta watsa rahoton cewa; mu'assisar fadakarwa ta garin Nanter na Faransa ta kaddamar da wata rana ta taimakwa domin gina cibiyar al'adu ta musulman Faransa. A ranar jiya ne ta ware wani daki na musamman domin kaddamar da wannan aiki na tara taimakon kudade domin gina wannan cibiyar ta al'adu ga musulmin kasar Faransa kuma wannan zai taimaka matuka gaya ga al'ummar musulmi da ke rayuwa a wannan kasa ta Faransa da kuma yada al'adunsu da ilimi gami da binkasa rayuwarsu ta zamantakewa.
555283