IQNA

A Koweiti A Bude Cibiyar Dindindim Ta Horar Da Limamai Da Masu Tabligi

Bangaren kasa da kasa; ma'aikatar da ke kula da harkokikn addini a kasar Koweiti a jiya ta bada labarin bude wata cibiya ta dindindim da za ta rika horar da kuma yaye limamai da masu yada addinin Musulunci a wannan kasa a larduna shidda na wannan kasa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta kasar Koweiti Kuna ta watsa rahoton cewa;
ma'aikatar da ke kula da harkokikn addini a kasar Koweiti a jiya ta bada labarin bude wata cibiya ta dindindim da za ta rika horar da kuma yaye limamai da masu yada addinin Musulunci a wannan kasa a larduna shidda na wannan kasa.Walid Shu'aib mai kula da harkokin masallatai a hukumar da ke kula da harkokin addini a wannan kasa ya fitar da wani bayani da ke bayyana wannan labari matakin ma'aikatar kula da harkokin addini da ilimi da burinta na kaddamar da wannan shiri na karfafa limamai da masu yada addini .

555300