IQNA

Kungiyar KasasHen musulmi Ta Amince Da Kuduri Take Hakkin Palasdinawa

15:58 - March 30, 2010
Lambar Labari: 1900863
Bangaren kasa da kasa; ikmalul Din Ihsan Uglu babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya fitar da wani bayani da a cikinsa yake nuna amincewar kungiyar hadin kan kasashen musulmi dangane da kudurin baya-bayan nan na komitin tsaro kan take hakkin Palsdinawa da HKI ke yi.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur;ani a nan jamhuriyar ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar gwamnatin hadeddiyar daular larabawa Wam ta watsa rahoton cewa komitin kare hakkin dan adam na majalisar dinkin duniya a zamansa karo na goma sha uku a Janeva na Suiziland a sabon kudurin day a fitar kan Haramtacciyar kasar Isra'ila da tat a yi ramuwar asarar da ta haddasawa Palsdinawa a yakin kwanaki ashirin da biyu kan Zirin Gaza. Dangane da wannan labari ikmalul Din Ihsan Uglu babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya fitar da wani bayani da a cikinsa yake nuna amincewar kungiyar hadin kan kasashen musulmi dangane da kudurin baya-bayan nan na komitin tsaro kan take hakkin Palsdinawa da HKI ke yi.


555504

captcha