IQNA

Hardar Juzi'I Biyar Shi Ne Sharadin Daukan Dalibi A Cibiyar Musulunci Ta Masar

Bangaren kasa da kasa; ma'aikatar da ke kula da harkokin addini a Masar ta bayyana cwa; hadace Juzi'I biyar na Kur'ani shi ne sharadin zama talibi a cibiyar al'adu ta Musulunci da ke karkashin wannan ma'aikata.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Mahit ta watsa rahoton cewa; ma'aikatar da ke kula da harkokin addini a Masar ta bayyana cwa; hadace Juzi'I biyar na Kur'ani shi ne sharadin zama talibi a cibiyar al'adu ta Musulunci da ke karkashin wannan ma'aikata. Mahmud Mahdi Zakzuk ministan da ke kula da harkokin addini a wannan kasa ta Masar dangane da wannan labari ya bayyana cewa; za a fara rubuta sunayen mata da maza masu bukatar yin karatu a wannan cibiya da ke karkashin ma'aikatar harkokin addini daga ranar sha biyu ga wannan watan na shamsiya wato jibi ke nan.

555551