IQNA

Radiyo Shi Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Yada Musulunci A Afrika

Bangaren kasa da kasa; mai kula da ofishin yada al'adun Iran a Zimbabwe ne ya bayyana cewa hanya mafi dacewa ta yada addinin Musulunci ita ce radiyo.
Muhammad Asadi Muwahid mai kula da ofishin yada al'adun Iran a kasar Zimbabwe a wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna dangane da tasirin yada addinin Musulunci da al'adu a wannan kasar ya bayyana cewa; hukumar da ke kula da yada al'adun Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun sha banban daga wannan yanki zuwa wannan yanki saboda banbancin yanayin al'adu da yanayin kasa.

556146