Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar kasar Katar Alraya ta watsa rohoton cewa; ; ma'aikatar da ke kula da harkokin addini a kasar Katar na rarraba kur'ani a masallatan kasar da cibiyoyin Musulunci da al'adu. Ma'aikatar harkokin addinin Musulunci ta yi niyar canja kur'anan da suka jima a masallatai da sabbi domin haka ya kara fito da masallatai da kuma karfin guiwa ga masu karatun Kur'ani a masallatai.Kuma kimanin kur'anai dubu dari bakwai ne za a rarraba a masallatai a kasar ta Katar.
556572