IQNA

Taron Gasar Karatun Kur'ani A Jami'ar Al-Mostafa (SAW)

16:08 - April 04, 2010
Lambar Labari: 1902305
Bangaren kur'ani; Za a fara gudanar da gasar karatun kur'ani da kuma harda na jami'ar Al-mostafa (SAW) a karo na goma sha shida a birnin Qom,
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga reshensa na birnin qom cewa, Za a fara gudanar da gasar karatun kur'ani da kuma harda na jami'ar Al-mostafa (SAW) a karo na goma sha shida a birnin Qom, taron gasar dai zai samu halartar daruruwan dalibai 'yan kasashen waje. Bayanin ya ci gaba da cewa bangaren da ke kula da harkokin kur'ani na jami'ar ne zai dauki nauyin shirya gasar. Daga cikin muhimman abubuwan da gasar za ta mayar da hankalii kansu a kwai karatu da kuma harda, run daga izihi na farko zuwa na biyar, sai kuma na goma zuwa ashirin, da kuma na ashirin zuwa talatin, sai kuma tajwidi. 555151
captcha