Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga shafin internet na ar.trend.az an habarta cewa; A fitowarsa ta farko a gidan talabijin, sabon shekhul Azhar Ahmad Tayyid ya bayyana cewa suna yin kokarin ganin sun hana yaduwar mazhabar shi'a a kasashen musulmi. Ahmad Tayyib wanda shi ne ya maye gurbin Tantawi, malamin day a shara wajen kare manufofin gwamnatin Masar tare da goyon bayan yahudawan sahyuniya kan ta'asar da suke tafkawa kan al'ummar musulmi, wanda ya mace a cikin makonnin da suka gabata, tare da shan kakkausar suka daga al'ummomin musulmi na duniya. Shi ma magajinsa ba a barsa a baya ba wahjen bin sahun magabacinsa. Furucin na Ahmad Tayyib ya zo a zantawarsa da talabijin din al'arabiyya ta gwamnatin Saudiyya, wadda ke kokarin yada rarraba kai tsakanin musulmi, tare da nuna kiyayya ga mazhabar ahlul bait. 556821