IQNA

An Kira Da A Samar Da Wata Hanya Ta Kididdige Mazhabobin Musulunci

16:09 - April 04, 2010
Lambar Labari: 1902319
Bangaren kasa d akasa; Limamin babban masallacin juma'a na yankin Katif, wanda yanki ne na mabiya mazhabar shi'a, ya yi kira da a san takamaimai adadin mazhabobin musulinci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, limamin babban masallacin juma'a na yankin Katif a kasar Saudiyya, wanda yanki ne na mabiya mazhabar shi'a, ya yi kira da a san takamaimai adadin mazhabobin musulinci. Ya kara da cewa mazhabobin musulunci suna da dama bai kamata wani bangare ya killace mazhabobi da shi mazhabarsa kawai, saboda bangaranci. Ya ci gaba da cewa addinin musulunci yana fadi matuka kuma fahimtar hakan tare da amincewa da hakan shi ne kawai hanyar kawo karshen rarrabar kawuna tsakanin al'ummar musulmi. 556594






captcha