Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga rshenta daga Jodan bayan ta nakalto daga jaridar Alra'ayi ta wannan kasa ta watsa rahoton cewa; : a jami'ar duniyar musulmi da ke bincike kan ilmomin Musulunci a Jodan ta fara wani nazari da bincike kan tasirin kur'ani a wakoki. Mahmud Huseini Alzahiri wani mai bincike dan kasar Jodan a lokacin da ke gabatar da bincikensa na kammala jami'a a bangaren shahadar doktora a jami'ar kasa da kasa da ke bincike kan ilimomin Musulunci a Jodan da ke birnin Oman fadar mulkin wannan kasa ya yi bincike ne kan tasirin kur'ani mai girma a cikin wakoki har zuwa karshen daular bani umayya.
557922