IQNA

A Tailand Ne Za A Kafa Karamar Jami'a Ta Nazarin Musulunci a Jami'ar Ayutaya

Bangaren nazari da ilimi: ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a kasar Tailand ne ya yi nuni da labarin kafa karamar jami'ar yin nazari kan Musulunci a jami'ar Ayutaya ta kasar Tailand nan bad a jimawa ba.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna daga reshenta da ke hukumar kula da yada al'adun Iran da kara dongon dangantaka tsakanin kasashen musulmi da musulmi ta watsa rahoton cewa; : ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a kasar Tailand ne ya yi nuni da labarin kafa karamar jami'ar yin nazari kan Musulunci a jami'ar Ayutaya ta kasar Tailand nan bad a jimawa ba. Jalal Tamla mai kula da ofishin yada al'adun Iran a kasar Tailand a lokacin day a ke ganawa da Hujjatul Islam Abu Turabi mukaddashin shugaban majalisar dokokin Iran ya yi masa bayani kan wannan labari da cewa bayan shekara guda na kokari da tashi fadi nan bad a jimawa ba a jami'ar Ayutaya za a bude wannan karamar jami'a.


557987