IQNA

Babu Wanda Zai Iya Hana 'Yan Shia Gudanar Da Sallar Jam'i

15:34 - April 06, 2010
Lambar Labari: 1903382
Bangaren kasa da kasa; Fitaccen malamin addinin nan na kasar Saudiyya Sayyid Muhammad Bakir Nasir ya bayyana cewa, babu wanda zai iya hana mabiya tafarkin iyalan gidan manzo yin sallar jam'i.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga tashar talabijin din Rasid an bayyana cewa, Fitaccen malamin addinin nan na kasar Saudiyya Sayyid Muhammad Bakir Nasir ya bayyana cewa, babu wanda zai iya hana mabiya tafarkin iyalan gidan manzo yin sallar jam'i. Malamin ya ce gwamnatin wahabiyan saudiyya tana yin iyakacin kokarinta wajen ganin ta hana mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) gudanar da harkokinsu na addini, da hakan ya hada da gudanar da sallolin jam'i, inda to wannan kam sun yi kadan. 557843



captcha