IQNA

Wutar Intifada Ta Uku Ce Za Ta Kona Yahudawan Sahayoniya

13:26 - April 07, 2010
Lambar Labari: 1903796
Bangaren siyasa: Habibi a yau ne a wani zama da jam'iyar Mualifatul Islami ya yi nuni da halin tankwalar fada da Yahudawan sahayoniya ke yi a yau da cewa Yahudawan sahayoniya na kokarin haddasa sabuwar gwagwarmaya ta Intifada ta hanyar mamaye Kudus kuma wutar Intifada ta uku ne za ta kona su.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga bangaren da ke kula da hulda da jama'a na jam'iyar ya watsa rahoton cewa; Habibi a yau ne a wani zama da jam'iyar Mualifatul Islami ya yi nuni da halin tankwalar fada da Yahudawan sahayoniya ke yi a yau da cewa Yahudawan sahayoniya na kokarin haddasa sabuwar gwagwarmaya ta Intifada ta hanyar mamaye Kudus kuma wutar Intifada ta uku ne za ta kona su. A yan kwanakin nan dai gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun tsananta kai hare haren wuce gonad a da iri da mamaye kan Palsdinawa a yankin zirin gaza da takurawa mutanan yankin da fuskantar maida martani.


558482
captcha