Bangaren siyasa da Zamantakewa; mai kula da ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a kasar Seraleyon a wani jawabi day a gabatar ga masallata a masallacin Nur a garin Faritawun bisa la'akari da halin tattalin arziki da tsananin talauci da musulmin wannan kasa ke fama da shi ce za a fara bincike kan dalilai da tushen Talauci a mahangar Musulunci.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta na hukumar da ke kula da yada al'adun Iran da kara dangantaka a ta Musulunci ta watsa rahoton cewa; mai kula da ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a kasar Seraleyon a wani jawabi day a gabatar ga masallata a masallacin Nur a garin Faritawun bisa la'akari da halin tattalin arziki da tsananin talauci da musulmin wannan kasa ke fama da shi ce za a fara bincike kan dalilai da tushen Talauci a mahangar Musulunci. Muhammad Rida Kazlasfi ya kara da cewa; koyarwa irin ta Musulunci na kiran musulmi da su rungumi ayyukan da suka shafi tattalin arziki da yakar duk wani abu makamancin talauci don haka ne ma addinin Musulunci ya bawa neman halaliya da aiki matsayin jihadi matsayi na daukaka.
558261