IQNA

Tattaunawar Fahimtar Juna Tsakanin Manyan Addinan Duniya

19:00 - April 07, 2010
Lambar Labari: 1903963
Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da wani zaman tattaunawa da bahasi tsakanin manyan addinai na duniya a birnin Sharjah.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran WAM an bayyana cewa; za a fara gudanar da wani zaman tattaunawa da bahasi tsakanin manyan addinai na duniya a birnin Sharjah, na haddadiyar daular larabawa da nufin samar da fahimtar juna tsakaninsu mai dorewa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daya daga cikin muhimman lamurra da suke da muhimmanci musulmi su mayar da hanakali kansu, ta yadda za a kawo karshe rashin fahimtar juna tsakanin mabiya addinai.558348

captcha