IQNA

An Kame Wani Mabiyin Ahlul Bait A Saudiya Saboda Sallar Jam'i

19:00 - April 07, 2010
Lambar Labari: 1903966
Bangaren kasa da kasa; Jami'an tsaron kasar Saudiyya a cikin kayan sarki sun kai farmaki a wata makaranta ta mabiya ahlul bait a garin khabr.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, gidan talabijin din Rasid ya habarta cewa, Jami'an tsaron kasar Saudiyya a cikin kayan sarki sun kai farmaki a wata makaranta ta mabiya ahlul bait a garin khabr, inda suka yi awon gaba da wani babban malamin addinin musulunci mabiyin ahlul bait Hassan Ali Makki, saboda ya jagoranci gudanar da sallar jam'i. Rahoton ya ci gaba da cewa wannan na daya daga cikin ayyukan ta'addancin da jami'an gwamnatin wahabiyawan saudiyya ke aikatawa kan mabiya tafarkin ahlul bait a kasar, wanda ake ganin cewa hakan ndanne hakkokinsu ne.558359


captcha