Bangaren al'adu da fasaha;cibiyar nazari da bada shawara ta Alzaituna a birnin Beirut fadar mulkin kasar Labanon a wani sabon littafinta da ta kaddama mai suna bincike kan tarihin al'adun birnin Kudus ta yi bayani da bincike kan tarihin al'adun wannan birni.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta na kasar Labanon bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Muhit ta watsa rahoton cewa;
cibiyar nazari da bada shawara ta Alzaituna a birnin Beirut fadar mulkin kasar Labanon a wani sabon littafinta da ta kaddama mai suna bincike kan tarihin al'adun birnin Kudus ta yi bayani da bincike kan tarihin al'adun wannan birni. Kuma shi wannan littafi an kaddamar da shi ne a lokacin da aka bayyana birnin kudus a matsayin fadar al'adu ta duniyar Larabawa a shekara ta daubu biyu da tara miladiya a kasar Labanon.
558709