Bangaren Internet: An bude wanisabon shafin yanar gizo na kur'ani mai tsarki da zai mayar da hankali wajen yada manufofin kur'ani da koyarwarsa a duniya ta hanyar yanar gizo wato internet.
A wata zantawa da ta hada daraktan shafin pars kur'an da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayyana cewa; Babbar manufar samar da wannan shafi ita ce bayar da dama ga masana kan harkokin kur'ani su bayar da tasu gudunmuwar da za su iya domin yada manufofin kur'ani zuwa ga sauran al'ummomin duniya. Daga cikin muhimman abubuwan da shafin ya mayar da hankali a kansu har da tattaunawa kan wasu daga cikin mas'aloli da kur'ani ya yi tsokaci a kansu, amma wasu suna juya su zuwa ga manufarsu, da nufin karkatar da fahimtar sauran al'ummomi daga hakikanin manufa ta kur'ani a kan wadannan mas'aloli. Ya ce bude wannan shafi zai bayar da dama wajen fito da hakikanin koyarwar kur'ani ga sauran al'ummomin duniya.559835