IQNA

Hauzar Najaf Na Shirin Karbar 'Yan Sunna Domin Karatu

20:43 - April 11, 2010
Lambar Labari: 1905552
Bangaren kasa da kasa; Limaminin juma'a a garin Najaf mai lafarma Sayyid Sadruddin Kubanji ya bayyana cewa, cibiyar ilimi ta birnin Najaf a shirye take ta karbi 'yan uwa 'yan sunna domin karatu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da yanakalto daga wata kafar yada labarai a kasar Iraki an bayyana cewa, Limaminin juma'a a garin Najaf mai lafarma Sayyid Sadruddin Kubanji ya bayyana cewa, cibiyar ilimi ta birnin Najaf a shirye take ta karbi 'yan uwa 'yan sunna domin karatu. Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin bayanin nasa sayyid kubanji ya jaddada wajabcin hada kai tsakanin dukkanin musulmi domin yi wa wannan addini hidima, kuma rashin wannan hadin kai na cutr da dukkanin bangarorin musulmi ne a duniya.559916
captcha