IQNA

Son Ahlul Bait (AS) Wajibi Ne A Kan Dukkanin Musulmi

20:42 - April 11, 2010
Lambar Labari: 1905559
Bangaren kasa da kasa; Ministan harkokin addini na yankin Kurdistan a kasar Iraki ya bayyana cewa, wajibi ne a kan dukkanin musulmi su so Iyalan gidan manzon Allah (ASW)
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin internet na Nun an habarta cewa, a jiya Kamil haji Ali ministan harkokin addini na yankin Kurdistan a kasar Iraki ya bayyana cewa, wajibi ne a kan dukkanin musulmi su so Iyalan gidan manzon Allah (ASW) ya ci gaba da cewa al'ummar yankin Kurdistan suna da wani matsayi na musamman wajen son iyalan gidan manzon Allah, wanda hakan ne ma ya sanya suke ziyartar wurare masu tsarki da ke cikin sassa na kasar Iraki tsawon shekaru. Ya ce yana kiran dukkanin musulmi na kasar Iraki da su hada kansu domin gina kasar da kuma yi mata hidima. 559872
captcha