Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin internet na nwiic an bayyana cewa, nan bad a jimawa ba za a fara gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki a cikin wannan wata na Afirilu a birnin Croun Point da ke cikin jahar Indiana a kasar Amurka. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daya daga cikin irin ayyukan da cibiyoyin mabiya addinin Musulunci a kasar Amurka ke gabatarwa da nufin kara karfafa gwiwar su kansu musulmin kasar, da kuma kara bayyana hakikanin koyarwar addinin Musulunci da ta zo cikin kur'ani. 559921