Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga wani shafin sadarwa na kasar Mauritania cewa, an gudanar da wani zaman taro kan harkokin tattalin arziki na kasashen musulmi a kasar Mauritania a matsayi na kasa da kasa, da ya samu halartar masana daga kasashen musulmi. Bayanin ya ci gaba da cewa mahalarta taron sun yi bahasi kan wasu muhimman lamurra da suka danganci matsayin tattalain arzikin kasashen musulmi da kuma yadda za a samu taimakekeniya a tsakaninsu. Bayanin y ace taron dai ga dukka alamu zai taimaka wajen farfado da dama daga wasu harkoki na tattalin arziki a kasashen musulmi.559991