Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Rasid a kasar saudiyya ya habarta cewa, Malaman addinin Musulunci kimanin 69 ne daga cikin mabiya mazhabar shi'a na kasar Saudiyya ne suka bukaci da a baiwa mabiya mazhabar shi'a 'yancin gudanar da hrkokinsu. Bayanin ya ci gaba da cewa, bisa la'akari da irin matakan takura wa mahukuntan wahabiya na gwamnatin Saudiyya ke dauka ne kan mabiya mazhabar shi'a, aka dauki wanna mataki domin sanar da su da ma duniya halin da ake ciki dangane da takura wa mabiya mazhabar shi'a da ake a kasar.560058