Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na kamfanin dillancin labaran marab cewa, Wani gungu wasu ashararn mutane da ba a san ko su wane ne ba sun sake wulakanta kur'ani mai tsarki a kasar Yeman, lamarin da ya jawo matsanancin fushin al'ummar kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa dubban mutane sun fito a kan manyan titunan birnin Mahrud na kasar domin nuna rashin amincewarsu da wannan mummunan aiki. A nasu bangaren malaman addini sun gudanar da wani zaman gaggawa domin dauakr matakan da suka dace. 560143