IQNA

A Kaliforniya Za A Gudanar Da Gasar Kur'ani

16:18 - April 12, 2010
Lambar Labari: 1906121
Bangaren kasa da kasa; a birnin Apaks na jahar kaliforniya ta Amerika za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma daga ranar sha takwas ga watan Ordevehesh na wannan shekara ta hijira shamsiya.
Bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Apexmosque cibiyar dake kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriya Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; ; a birnin Apaks na jahar kaliforniya ta Amerika za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma daga ranar sha takwas ga watan Ordevehesh na wannan shekara ta hijira shamsiya. Wannan gasar ta karatun Kur'ani a jahar ta Kalifornoiya an kasa ta kashi kashi kuma gida gida kama daga kananan yara har zuwa manya da matasa.


560764

captcha