Bayan ta nakalto daga majiyar labarai APP Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; malamai musulmi a Birtaniya sun bukaci musulmi a kasar da su shiga cikin zabe da za a gudanar a fadin kasar aranar sha shidda ga watan Ordevehesh mai kamawa. A cikin wani bayani da hadin guiwar malaman juma'a a wannan kasa suka fitar ne ya bukaci musulmin da su halarci wannan zabe domin kare hakkinsu na zabe a fadin kasar.
560909