IQNA

ZamanTaro Dangane Da Batun Palastinu A Kasar Faransa

19:14 - April 12, 2010
Lambar Labari: 1906167
Bangaren kasa da kasa; Cibiyar gudanar da bincike kan ilimin addinin musulunci ta kasar Faransa ta shirya gudanar da wani zaman taro Da ke yin bahasi kan sha'anin palastinu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani rahoto da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran saphirnews an bayyana cewa, Cibiyar gudanar da bincike kan ilimin addinin musulunci ta kasar Faransa ta shirya gudanar da wani zaman taro Da ke yin bahasi kan sha'anin palastinu. Bayanin ya ci gaba da cewa, taron ya mayar da hanakali kan abubuwan da suka faru a lokacin da yahudawan sahyuniya suka kaddamar da yaki kan al'ummar Gaza a shekarar da ta gabata.560312


captcha