IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Shekara-Shekara A Libya

19:18 - April 12, 2010
Lambar Labari: 1906168
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka saba gudanarwa a kowace shekara a kasar Libya
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar Alfajr jaded ta kasar Libya cewa, an fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka saba gudanarwa a kowace shekara a kasar Libya, wadda ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar kan shirya gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan daya daga cikin irin nau'oin gasar da wannan ma'aikata kan shirya gudanarwa a kasar, kuma yanzu haka mahardata da makaranta daga sassa daban-daban na kasar ne suke halaratr wannan taron gasa abirnin Tripoli.560475


captcha