Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar kasar Masar alyau sabi cewa, jaridar kasar Amurka Cristian Science Monitor ta habarta cewa, farin jinin da jami'ar Azhar ta kasar Masar take da shi a lokutan baya ya ragu matuka a duniya. Bayanin ya ci gaba da cewa babban dalilin hakan ba ya rasa nasaba da yadda jami'ar da malamanta suka zama 'yan amshin shatan gwamnatin kasar, musamman ma dai shugaban kasar Husni Mubarak, wanda ya zama shi ne wuka shi ne nama a cikin dukkanin harkokin wannan babbar jami'a.560558