IQNA

19:15 - April 12, 2010
Lambar Labari: 1906176

A Karo na Shida Za A Gudanar Da Taro Kan Saka Hannayen Jari

Bangaren kasa da kasa; Ana shirin gudanar da wani zaman taro kan harkokin saka hannayen jari a mahangar addinin musulunci a kasar Bahrain

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin kafar yada labarai na mega cewa, Ana shirin gudanar da wani zaman taro kan harkokin saka hannayen jari a mahangar addinin musulunci a kasar Bahrain, tare da yadda musulunci ya amince a karbi bashi. Bayanin ya ci gaba da cewa, taron za a gudanar da shi ne a mtsayi na kasa da kasa, kuma zai mayar da hankali ne dangane da yadda ya kamata musulmi su karfafa junansu wajen saka hannaayenjari domin samun ci gaban harkokin tattalin arzikin kasashen musulmi. 560698


captcha