Bangaren al'adu da fasaha; zangon fadakarwa ta addini kan aure kan mata da ke Darul Ifta'a a birnin Trablus na arewacin Labanon.
Daga kasar Labanon cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: zangon fadakarwa ta addini kan aure kan mata da ke Darul Ifta'a a birnin Trablus na arewacin Labanon. A babban zauren taro na Darul Ifta'a ne na wannan birni aka gudanar da wannan taro inda aka samu halartar yan mata ashirin yan makaranta inda aka yi masu bayani kan muhimmanci da alfanon aure da zabar miji da kuma alfanon haka a rayuwa da abubuwa na addini day a kamata a yi la'akari da su wajen zaben abokin zaman aure da kuma taimakon uwaye wajen zaban miji da fifita mai addini kan waninsa.
561301