Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin watsa labarai na cibiyar yada addinin musulunci da ke birnin Tehran an bayyana cewa, Daya daga cikin fitattun malaman tarihi na Tehran ya fadi cewa, sake rubuta tarihin musulunci musamman muhimman da suka da kowa bukata wajibi ne. Ya ci gaba da cewa wannan wajibi da ya hau kan malaman tarihin musulunci, domin ta hakan ne kawai za a san muhimman abubuwa da suka faru musamman ma a lokacin halifancin abasiyawa. 561440