IQNA

19:55 - April 13, 2010
Lambar Labari: 1906806

Za A Kaddamar Da Wani Gini Na Tunawa Da Imam Mahdi (AJ)

Bangaren kasa da kasa; Za a kaddamar da dora tubalin wani gini na tunawa da Imam Mahdi (AJ) a birnin Karbala mai alfarama na kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wani rahoto da aka buga a shafin yanar gizo na nun an bayyana cewa, Za a kaddamar da dora tubalin wani gini na tunawa da Imam Mahdi (AJ) a birnin Karbala mai alfarama na kasar Iraki, wanda wasu cibiyoyin addini suka dauki nauyin gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa cibiyoyin za su gudanar da wanna aiki ne tare da hadin gwiwa da mahukuntan birnin na karbala mai alfarma. 561341




captcha