Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin yada labarai na sfu.ca ya buga shafinsa cewa, babbar cibiyar mabiya addinin musulunci ta kasar Canada ta shirya gudanar da wani taro na bayar da horo dangane da addinin muslunci da kuma samun masaniya kansa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daya daga cikin muhimman ayyuka da wannan cibiya ke daukar nauyin gudanarwa da nufin kara wayar da kan wadanda ba musulmi a kasarba su fahimci hakikanin koyarwarsa. 561378